Bangaren kasa da kasa, haratacciyar kasar Isra'ila na ci gaba da kaddamar da harin ta'addanci kan fararen hula palastinawa mazauna yankin zirin Gaza tare duk kuwa da cewa hakan ba a boye a ke yinsa ba amma kuma babu wata kasa daga cikin kasashen yammacin turai masu da'awar kare hakkin bil adama da t ace uffan kan hakan.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar alalam cewa, haratacciyar kasar Isra'ila na ci gaba da kaddamar da harin ta'addanci kan fararen hula palastinawa mazauna yankin zirin Gaza tare duk kuwa da cewa hakan ba a boye a ke yinsa ba amma kuma babu wata kasa daga cikin kasashen yammacin turai masu da'awar kare hakkin bil adama da ta ce uffan kan wannan ta'addanci.
Yawan Palasdinawan da suka yi shahada sakamakon hare haren da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai kan yankin Zirin Gaza sun haura zuwa bakwai.
Majiyoyin tsaro da na asibiti da suke yankin Zirin Gaza sun tabbatar da cewa; Sakamakon hare haren wuce gona da iri da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai ta sama da kasa kan yankin Zirin Gaza a cikin sa'o'i 24 da suka gabata; Palasdinawa 7 ne suka yi shahada tare da jikkata wasu da dama.
A gefe guda kuma bangaren sojin Qassam take karkashin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya sanar da harba makamai masu linzami kirar Grad har guda 10 kan matsugunan yahudawa 'yan kaka gida ciki har da wani barikin sojin h.k.Isra'ila a matsayin mai da martani kan hare haren da sojojin gwamnatin h.k.Isra'ila ke kai wa kan yankin Zirin Gaza.
1032290