Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta press tv cewa, kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa da suka hada da kungiyar afuwa ta duniya duk sun yi Allawadai da kisan da mahukuntan kasar Saudiyya suka yi wa wasu Iraniyawa ba tare da wani hukunci ba a garin Dammam da ke gabacin kasar tare da bayyana hakan da cewa mataki na siyasa tsantsa.
A bangare guda kuma daya daga cikin manyan 'yayan gidan sarautar Saudiyya wato Talal Ben Abdul'Aziz ya ce Majalisar da ke nada sabon Yerima da kuma sauran al'amurran gudanarwa na gidan sarautar kasar ba ta da wani muhimmanci domin kuwa ta daina taka wata rawa wajen zaben yerima mai jiran gadon sarautar kasar kamar dai yadda aka saba.
A wata zantawa da jaridar Alqudusul-Arabiyya ta harshen Larabci da ake bugawa a birnin Landan, Talal Ben Abdul Aziz wanda 'yayan kishiya ne shi da sarkin da ke kan karagar mulkin kasar Abdullah Ben Abdul-Aziz ya bayyana cewa abu ne mai wuya Majalisar ta ci gaba da yin mubaya'a ga sabon yerima mai jiran gado da aka nada a shekaranjiya a kasar wato Salman Bin Abdul Aziz, yana mai cewa an nada sabon Yeriman ne ba tare da an tuntubi mambobin Majalisar da ke da hurumin yin hakan ba.
Talal Ben Abdul Aziz ya ce wannan matsala ta rashin mutunta matsayin wannan Majalisa ta faro ne tun a lokacin da aka nada Yeriman da Allah ya yi wa rasuwa a shekaranjiya Nayef Ben Abdul'Aziz. Ita dai wannan Majalisa mai zaben yerima an kafa ta ne a 2006, kuma kowanne daga cikin zuriyar 'yayan sarkin Saudiyya na farko wato Abdul Aziz na da wakili daya a cikinta, kuma su ne ke haduwa domin nada yerima mai jiran gado.
1033492