IQNA

Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Na Ci Da Kai Hari Kan Al’ummar Gaza

14:04 - June 21, 2012
Lambar Labari: 2351378
Bangaren kasa da kasa, Sakamakon shiru da kungiyoyin kasa da kasa gami da gwamnatocin kasashen Larabawa suka yi, yankin Palasdinawa na Zirin Gaza yana ci gaba da fuskantar hare haren wuce gona da iri daga sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila, jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai hare hare kan yankin Zaitun da gabashin garin Gaza gami da garin Rafah a jiya laraba, lamarin da ya yi sanadiyyar shahadar Palasdinawa biyu.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Muslim-village cewa, rahotonnin da suke fitowa daga yankin na Zirin Gaza suna bayyana cewa; a jiya laraba jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suna ta shawagi a sararin samaniyar yankin Zirin Gaza da nufin murkushe duk wani yunkurin 'yan gwagwarmayar Palasdinawa na mai da martani kan hare haren zaluncin da suke fuskanta, kuma har ya zuwa yanzu babu labarin batun kulla wata yarjejeniyar dakatar da bude wuta tsakanin Palasdinawa da haramtacciyar kasar ta Isra'ila.
A sanarwar da ma'aikatar harkokin cikin gida da na tsaro da suke karkashin zababbiyar gwamnatin Palasdinawa da ke yankin Zirin Gaza suka fitar a jiya laraba; sun yi Allah wadai da hare haren zaluncin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke kai wa kan yankin Zirin Gaza ta sama da kasa, tare da jaddada cewar jami'an tsaron Palasdinawa da kungiyoyin gwagwarmaya a yankin zasu dauki matakan mai da martani kan wannan hare hare na wuce gona da iri da suke fuskanta.
Har ila yau sanarwar ta fayyace cewar manufar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila na tsananta kai hare hare kan yankin Zirin Gaza a wannan lokaci ita ce; kara janyo rudani da rikici da zasu kara janyo tabarbarewan matakan tsaro a dukkanin yankin gabas ta tsakiya da kuma kokarin sake aiwatar da kisan kiyashi kan Palasdinawa kamar yadda ya faru a shekara ta 2008, don samun damar kara shimfida bakar siyasarsu ta zalunci da kwace a yankunan Palasdinawa.
A hare haren zaluncin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kaddamar kan yankin Zirin Gaza a cikin kwanaki 22 na karshen shekara ta 2008, Palasdinawa kimanin 1500 da suka hada da mata da kananan yara ne suka rasa rayukansu, wasu dubbai kuma suka jikkata tare da lalata duk wasu wajaje masu muhimmanci da suke yankin da nufin kara durkusar da Palasdinawa.
A matakin farko da 'yan gwagwarmayar Palasdinawa suka dauka na mai da martani kan hare haren zaluncin da suke fuskanta daga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a wannan lokaci; bangaren sojin Izzuddeen Qassam da ke karkashin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya harba makamai masu linzami kirar Grad kan matsugunan yahudawa 'yan kaka gida ciki har da barikin sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.
1033349






captcha