Bangaren kasa da kasa, babban sakataren cibiyar kusanto da mazhabobin muslunci ta duniya ya bayyana cewa babban nauyi ne da ya rataya a kan jagororin mabiya addinai na duniya da su taka gagarumar rawa wajen samar da sulhu da fahimtar juna tsakanin al’ummomin duniya baki daya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Ayatollah Taskhiri babban sakataren cibiyar kusanto da mazhabobin muslunci ta duniya ya bayyana cewa babban nauyi ne da ya rataya a kan jagororin mabiya addinai na duniya da su taka gagarumar rawa wajen samar da sulhu da fahimtar juna tsakanin al’ummomin duniya baki daya domin ta haka ne kawai za a iya kaiwa ga wannan buri.
Kungiyar lauyoyi musulmi sun gudanar da wani zama na musamma a birnin maskat fadar mulkin kasar Oman domin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci halin da ake ciki yanzu haka a wasu kasashen larabawa da kuma irin gudunmawar da za su iya bayarwa domin kare hakkokin mutane, duk kuwa d cewa ra’ayoyi kan boren larabawa sun sha banban.
professor Khan Martos wani malami a jami’ar Compol da ke birnin Madrid ya bayyana cewa fadakar da aka fara samu a cikin kasashen larabawa ta fara game sauran kasashe musamman ma dai na mabiya addinin muslunci daga cikinsu inda suke fara neman hakkokinsu na siyasa da aka haramta musu.
An ware wasu makudan kudade da suka kai dalar Amurka miliyan saba’in domin gudanar da ayyuak na musamman da suka shafi muslunci a kasar Malzia a cikin kasafin kudi na wannan shekara da nufin bunkasa harkokin addinin muslunci a fadin kasar, wadda take daya daga cikin kasashen musulmi.
1034447