Bangaren kasa da kasa, mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah a kasar Mali sun gudanar da zama domin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci harkokin da suke gudanarwa na karantarwa da ilimi da ayyukan al’adu da sauransu kamar dai yadda suka saba a yi a kowace shekara.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah a kasar Mali sun gudanar da zama domin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci harkokin da suke gudanarwa na karantarwa da ilimi da ayyukan al’adu da sauransu kamar dai yadda suka saba a yi a kowace shekara a birnin Bamako fadar mulkin kasar da sauran yankuna.
Da dama daga cikin masana sun ammanar cewa kasashen yammacin turai na hankoron ganin sun kawo yakin basasa a cikin kasar Syria, ta yadda hakan zai baiwa haramtacciyar kasar Isra’ila ci gaba da cin karenta babu babbaka a yankin wadda kuma take fuskantar barazana daga kasasar ta Syria a kowane lokaci saboda matsayinta na kishin al’ummar larabawa.
Kasar Syria ita kadai ce daga cikin kasashen larabawa da haramtacciyar kasar Isra’ila take kallonta a mtasyin barazana, saboda haka faduwar Bashar Asad babbar riba ce gare tasaboda yin hakan zai ba ta damar ci gaba da aiwatar da abin da tashirya na samar wanoi sabon yanayi a yankin gabas ta tsakiya baki daya, ta yadda za ta zama babbar daula mai cikakaen iko kan sauran dukaknin kasashen yankin.
1035325