Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, lokutan da suka gabata kasar Masar ta kasance kan gaba ta fuskacin karatu da hardar kur’ani mai tsarki amma a halin yanzu Iran ta yunkuro kuma ta shiga gaba wajen gabatar da shirin gasar karatu da hardar kur’ani mai tsar a matsayi na kasa da kasa kamar dai yadda take a kowace shekara har tsawon shekaro ashirin da tara da suka gabata a nan birnin Tehran, fadar mulkin jamhuriyar muslunci ta Iran.
Gudanar da wani zaman taro domin samar da fahimtar juna tsakanin mabiya ddinin muslunci da kuma mabiya addinin kiristanci da ma sauran addinai a birnin London na kasar Birtaniya tare da halartar malamai da masana daga sassa na kasar da ma wasu kasashen turai da suke makwaftaka da ita.
masu neman sauyi a kasar Bahrain sun yi kakkausar suka da yin Allawadai da taron da shugabannin kasashen larabawa suka gudanar a kasar Iraki saboda yadda zaman taron ya kawar da idonsa kan abin da yake faruwa a kasar na cin zarafin fararen hula masu zanga-zangar lumana a fadin kasar ta Bahrain.
Gungun 14 ga watan Fabrairu da ke jagorantar boren neman sauyi a Bahrain, wanda dukkanin bangarori na kasa da kasa suka tabbatar da cewa sama da kashi tamanin cikin dari ne suke gudanar da wannan bore, gungun ya fitar da wani bayani da ya yi kakakusar suka a cikinsa, dangane da yadda wadannan kasashen suke nuna banbanci tsakanin al’ummomin larabawa.
Masu neman sauyi a kasar Bahrain sun yi kakkausar suka da yin Allawadai da taron da shugabannin kasashen larabawa suka gudanar a kasar Iraki saboda yadda zaman taron ya kawar da idonsa kan abin da yake faruwa a kasar na cin zarafin fararen hula masu zanga-zangar lumana domin neman hakkokinsu.
1033659