IQNA

Makarancin Kur’ani Na Kasar Turkiya Ya Yaba Da Gasar Kur’ani A Kasar Iran

17:08 - June 23, 2012
Lambar Labari: 2352590
Bangaren kasa da kasa, makarancin kur’ani mai tsarki daga kasar Turkiya ya yaba da yadda ya ga gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki na gudana a jamhuriyar muslunci ta Iran kamar dai yadda ya sheda ma wasu daga cikin kafofin yada labarai da suka zanta da shi a wannan gasa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa cewa, wani makarancin kur’ani mai tsarki daga kasar Turkiya ya yaba da yadda ya ga gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki na gudana a jamhuriyar muslunci ta Iran kamar dai yadda ya sheda ma wasu daga cikin kafofin yada labarai da suka zanta da shi a wannan gasa da aka kammala a jiya.
kungiyar kare hakkokin bil adama takasar Bahrain ta gudanar da wani taron baje koli na ta’asar da masautan kasar Bahrain suke tafakawa kan fararen hular masu neman sauyi na siyasa da harkokin mulki na kasar baki daya.
A yayin gudanar da taron baje kolin masana da mamalan addini da kuma lauyoyi gami da masu rajin kare hakkin bil adama na kasar Bahrain da Lebanon da wasu kasashe sun halarci wannan baje koli da aka shirya a birnin na Beirut, domin nuna goyon bayansu ga al’ummar Bahrain da ake zalunta mafi sharrin zalunci.
Kungiyar kare hakkokin bil adama takasar Bahrain da ta gudanar da taron na baje koli na ta’asar da masautan kasar Bahrain suke tafakawa kan fararen hular masu neman sauyi na siyasa da harkokin mulki a kasar, ta jaddada wajabcin ci gaba da goyon bayan fararen hula na kasar.
1035274




captcha