Bangaren kasa da kasa, ministan ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar Indonesia ya bayyana cewa suna niyar kara fadada makarantun addinin muslunci a kasar kasantuwar kara yawan jama’a da ake samu kuma makarantun suna kara karanci wanda a cewarsa ba yawansu ne kawai ke da muhimamnci ba har ma da kyautata tsarin karantunsu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa a gabacin Asia cewa, Suryardarma Ali ministan ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar Indonesia ya bayyana cewa suna niyar kara fadada makarantun addinin muslunci a kasar kasantuwar kara yawan jama’a da ake samu kuma makarantun suna kara karanci wanda a cewarsa ba yawansu ne kawai ke da muhimamnci ba har ma da kyautata tsarin karantunsu wanda zai taimaka matuka.
Gudanar da wani shiri na musamman dangane da bayar da horo ga limaman masallatai na kasar Jamus, wanda jami’ar Snaburg ta kasar za ta dauki nauyin aiwatar da shi tare da hadin gwai da cibiyoyin mabiya addinin muslunci, hakan na da matukar alfanu ga musulmi.
A halin yanzu akwai limaman masallatai sama da dubu takwas a fadin kasar Jmaus, kuma akasarinsu mutanen kasar Turkiya dasuke je kasar daga bangaren gwamnatin Turkiya, wadanda ba su da cikakkiyar masaniya kan harshen jamusanci.
Keta lafarmar kur’ani mai tsarki mummunan aiki ne da ya yi hannun riga da dukkanin dabiu na ‘yan adamtaka wanda kuma shi ne abin da duniya take ganin ana yi yanzua cikin kasashen yammacin turai da sunan ‘yancin fadar albarkacin baki ko bayyana ra’ayi. 1036656