Bangaren siyasa, ma'aikata harkokin wajen jamhuriyar muslunci ta Iran ta taya zababben shugaban kasar Masar Muhammad Mursi murnar lashe zaben day a yi zagaye na biyu wanda hakan ya bas hi damar zama shugaban kasar na farko bayan kawar da gwamnatin kama karya ta tsohon shugaban kasar Husni Mubaraka shekarar da ta gabata.
Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanr gizo na ma'aikatar harkokin wajen Iran cewa, ma'aikata harkokin wajen jamhuriyar muslunci ta Iran ta taya zababben shugaban kasar Masar Muhammad Mursi murnar lashe zaben day a yi zagaye na biyu wanda hakan ya bas hi damar zama shugaban kasar na farko bayan kawar da gwamnatin kama karya ta tsohon shugaban kasar Husni Mubaraka shekarar da ta gabata bayan yunkurin al'ummar kasar.
Zababben shugaban kasar Masar Mohamed Morsi, ya ce zai mutunta yarjeniyoyin kasa da kasa wanda kasar Masar ta sanya hannu a kai, yana cewa za mu kiyaye yarjeniyoyi da kasar ta amince da su tun farko. A cikin mahimman yarjejniyoyin da kasar ta Masar ta sama hannu akwai ta zaman lafiya da HKI tun 1979.
Da farko Jam'iyar yan uwa musulmi, sun ce za su sake duba yarjejeniyar da aka yi da HKI idan har kasar Amurka ta janye tallafin da ke ba kasar. A na ta bangare HKI ta yaba ma tafarkin demokaradiyar da kasar ta Masar ta shiga da ya bada dama ga M Morsi ya zama shugaban kasa, tare da fatan dorewar huldar dake tsakanin kasashen biyu. A wata sanarwa ta ofishin fraministan HKI sun ce kasar na fatan ci gaba da hulda da kasar Masar karkashin yarjejeniyar.
Sabon shugaban dake samun sakonnin barka daga ko'ina ya yi fatan alummar kasar za su hada kai wuri guda domin a cewarsa tare da hadin kai ne za a iya fita daga cikin mawuyacin hali ya bayyana haka ne a cikin jawabinsa na farko day a gabatar a matsayinsa na zababben shugaban kasa.
1037479