IQNA

Babba Sakataren Kungiyar kasashen Musulmi Ya Yaba Da Zaben Muhammad Mursi

17:59 - June 27, 2012
Lambar Labari: 2356042
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi Ihsan Auglo ya yaba da zaben Muhamamd Mursi da al'umamr kasa Masar suka yi tare da bayyana hakan da cewa shi ne hakikanin mulki na demokradiyya da kasar ta fada shedawa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi Ihsan Auglo ya yaba da zaben Muhamamd Mursi da al'umamr kasa Masar suka yi tare da bayyana hakan da cewa shi ne hakikanin mulki na demokradiyya da kasar ta fada shedawa, tare da fatan kasar ta samu kwanciyar hankali.
Zabebben shugaban kasar Masar Muhammad Mursi ya fara tattaunawa da manya manyan jami'an sojojin kasar kan batutuwan da suka shafi kafa sabuwar gwamnati da kuma makomar majalisar dokokin kasar wanda sojojin suka rusa jim kadan kafin abayyana sakamakon zaben shugaban kasa.
Sami Essawi wani mai Magana da yawon shugaban ya bayyana a yau talata cewa, shugaba Mursi zai nada mataimakan shugaban kasa guda 6, wanda zai hada da mace guda, kirista guda da kuma wasu daga cikin jam'iyyun adawar kasar.
A jiya litinin ne Muhammad mursi ya je fadar shugaban kasa ya zagaya sannan ya tafi ma'aikatar tsaron kasar inda ya fara tattaunawa da manya manyan jami'an sojoji masu mulkin kasar., shugaba Muhammad Mursi ya sauka daga mukaminsa na shugaban kungiyar ikhwanul muslimin bayan da hukumar zaben kasar ta bada sanarwan cewa shi ne ya lashe zaben shugaban kasar masar, don ya zama shugaban dukkan mutanen kasar Masar.
Tuni dai kungiyar ta maye gurbin Mursi da Essam el-Erian a matsayin shugaban wucin gadi, kafin zaben shugaba na din din din nan gaba.
1038929


captcha