Bangaren kasa da kasa:shugaban yan sanda a kasar Suiziland ya bada labarin kamawa da yin awangaba da wani matashi dan kasar mai shekaru talatin da bakwai a duniya a daidai lokacin da yake ingiza mutanan kasar kai wa masallaci hari a shafin Tweiter na ake bawa jama'a bayyana ra'ayi da abubuwa da suka shafi zamantakewa amma sai ya yi mafani da wannan dama ta mummunar hanya ta ingiza jama'a.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; shugaban yan sanda a kasar Suiziland ya bada labarin kamawa da yin awangaba da wani matashi dan kasar mai shekaru talatin da bakwai a duniya a daidai lokacin da yake ingiza mutanan kasar kai wa masallaci hari a shafin Tweiter na ake bawa jama'a bayyana ra'ayi da abubuwa da suka shafi zamantakewa amma sai ya yi mafani da wannan dama ta mummunar hanya ta ingiza jama'a.Bayan an nakalto daga majiyar labarai ta TDG an watsa rahoton cewa: yan sandan kasar Suiziland sun fitar da wani rahoto day a shafi harkokin tsaro cewa; Alaksandr Moler matshi dan shekaru talatin da bakwai da haifuwa mazaunin zurikh an kama shi da yin awangaba das hi karkashin saminsa da laifin ingiza jama'a na kai wa wani masallaci hari .Kuma daga cikin mummunan sakon ya yi ta aikewa sun shafi katamta harin da aka kai wa gurin ibadar yahuda a watan nowamban shekara ta dubu daya da dari tara da talatin da takwas da ake yiwa lakabi da daren fasa gilashi da cewa irin wannan hari ne za a kai wa masallaci .A daidai wannan lokaci da harkokin tsaro da zaman lafiya yayi kamari a lafiyar turai ana samin irin wannan hali na takalar fada da nuna katran tsana kan addinin musulunci da musulmi a nahiyar turai.
1039606