Kmafanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga bangaren yada labaransa na nahiyar Afirka cewa ana ci gaba da gudanar da wani zaman taro Niyambo birni mafi girma mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah suke zaune a cikinsa a kasar kan matsayin Imam Hujjah (AS) da kuma saninsa bisa ruwayoyi na iyalan gidanzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.
Yanzu haka ana ci gaba da gudanar da taron baje koli na kasa da ake yi a kasar Pakistan an nuna wasu daga cikin manyan kwafin kur’ani mai tsarki a ginin babbar cibviyar yada al’adun muslunci da ke birnin Lahor, birnin na boyi ta fuskancin girma da kuma harkokin tattalin arziki na kasar Pakistan.
A wajen taron na bajen kolin an nuna kwafi-kwafi na kur’ani mai tsarki wadanda aka rubuta da hannu a kasashen musulmi daban-daban, haka nan kuma wadanda aka buga su a kasashen musulmi, da nufin kara fito da matsayin wannan littafi mai tsarki, tare da bayyanawa duniya cewa matsayinsa yana damfare ne da rayuwar mabiya addinin muslunci, domin ya zama hannunka mai sanda ga masu keta alfarmarsa.
Gudanar da taron baje koli na kasa da ake yi a kasar Pakistan inda ake nuna wasu daga cikin manyan kwafin kur’ani mai tsarki a ginin babbar cibiyar yada al’adun muslunci da ke birnin Lahor na kasar, na dag acikin muhimamn ayyuka da gwamnatin kasar pakistan ke aiwatarwa akowace shekara.
1040560