Bangaren siyasa, ‘yan majalisar dokokin jamhuriyar muslunci ta Iran sun aike da sakon taya murna ga sabon shugaban kasar Masar wanda al’ummar kasar suka zaba amatsayin zababben shugaba tare da yi masa fatan alkhairi da kuma samun nasara wajen gudanar da ayyukan da ke gabansa na jagorantar al’ummar kasar Masar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, ‘yan majalisar dokokin jamhuriyar muslunci ta Iran sun aike da sakon taya murna ga sabon shugaban kasar Masar wanda al’ummar kasar suka zaba amatsayin zababben shugaba tare da yi masa fatan alkhairi da kuma samun nasara wajen gudanar da ayyukan da ke gabansa na jagorantar al’ummar kasar Masar wadda daya ce daga muhimamn kasashen musulmi.
Wani labarin an daban wasu daruruwan mutane a cikin fushi sun afka kan babban ofishin hukumar zabe da ke birnin Bingazi na kasar Libya domin nuna rashin amincewarsu da zaben da ake shirin gudanarwa a kasar da mako guda mai zuwa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa mutanen sun kone ofishin hukumar zaben da dukkanin abin da ke cikinsa, kamar yadda suka daga kwalaye da kyallaye da aka yi rubutun kansu da ke bayyana shugaban majalisar wucin gadin kasar Mustafa Abduljalil a matsayin maha’inci, sun kuma fitar da wasu na’urorin kwamfuta da takardun zabe suka banka musu wuta a gaban jama’a.
A cikin watan Mayun da ya gabata ne majalisar yankin Barka da ta shelanta kwarkwryan cin gishin kai a gabacin Libya, ta kirayi al’ummomin yanki da kada su kada kuri’a a zaben ‘yan majalisar da za a gudanar a ranar 7 wannan wata Yuli, saboda abin da suka kira rashin adalci wajen bayar da kujeru ga yankunan kasar.
1042244