Bangaren kasa da kasa, sama da makaloli 500 aka aike das u zuwa ga taron da ake gudanarwa a matsayi na kasa da kasa a babban birnin jamhuriyar muslunci tare da halartar masana daga sassa na duniya da adadinsu yah aura dubu daya da dari biyu kamar dai yadda bangarorin da suke daukar nauyin taron suka bayyana ga manema labarai.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, sama da makaloli 500 aka aike das u zuwa ga taron da ake gudanarwa a matsayi na kasa da kasa a babban birnin jamhuriyar muslunci tare da halartar masana daga sassa na duniya da adadinsu yah aura dubu daya da dari biyu kamar dai yadda bangarorin da suke daukar nauyin taron suka bayyana ga manema labarai a yammacin yau.
Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran sannan Dakta Sa'id Jalili ya aike wa babbar jami'ar siyasar waje ta kungiyar tarayyar Turai sannan kuma shugabar tawagar manyan kasashen duniyar a tattaunawar Madam Catherine Ashton da wata wasika inda ya ja kunnen kasashen yammaci dangane da abin da zai biyo bayan amfani da hanyoyin da ba su dace ba wajen mu'amala da kasar Iran. Har ila yau a cikin wasikar, Dakta Jalilin ya yi ishara da shawarar da Iran ta bayar a tattaunawar da ta yi da turawan a birnin Mosko inda ya sake jaddada cewa Iran kamar kullum a shirye take taci gaba da tattaunawar da ta ginu bisa amfani da hankali da girmama juna.
Jami'an Iran dai sun sha bayyana aniyarsu ta aiki tare da manyan kasashen duniyan wajen kawo karshen duk wani rashin fahimta da ya kunno kai a bangaren shirin nukiliyanta na zaman lafiya inda tsawon wadannan shekaru na tattaunawa ta tsaya kan wasu batutuwa guda uku a matsayin siyasarta a wannan fagen da suka hada da tsayin daka wajen tabbatar da hakkinta, amfani da hankali da girmama juna da kuma aiki a kas.
Dubi cikin tattaunawar baya-bayan nan tsakanin Iran da kasashen kungiyar 5+1 tun daga tattaunawar Istanbul na kasar Turkiya zuwa birnin Mosko na kasar Rasha ana iya bakar aniyar da manyan kasashen duniyar suke da ita kan Iran. A matsayin misali a tattaunawar farko ta birnin Istanbul, manyan kasashen duniya sun ki su amince da hakkin da Iran take da shi na amfani da makamashin nukiliya ta hanyar zaman lafiya da Iran take da shi. To amma sakamakon tsayin dakan Iran daga karshe dai a tattaunawar Istanbul ta biyu Madam Ashton din ta bayyana cewar manyan kasashen duniya za su girmama hakkin da Iran take da shi na mallakan fasahar nukiliya karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman kare dangi NPT, haka nan kuma da aiki tare bugu da kari kan yin watsi da batun aiwatar da kudurin kwamitin tsaron MDD kan Iran a matsayin sharadin sake tattaunawa da Iran.
1049553