Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar rasid cewa, mahukuntan wahabiyawan Saudiyya suna wariya ga al’ummar kasar mazauna yankunan gabaci kasantuwarsu mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah duk kuwa da cewa dukkanin arzikin da ake takama da shia akasar ana fitar da shi daga yankunansu da ke gabacin kasar da tashahara a duniya wajen arzikin manfetur.
Gwamnatin kasar Rasha ta nuna matukar damuwa dangane da yadda mahukuntan Saudiyya suke yin amfani da karfifiye da kima wajen murkushe fararen hula masu zanga-zangar a yankunan gabacin kasar.
Babban jami’I mai kula da harkokin kasashen larabawa a ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Qostine Dolgov ya fadi jiya a gaban manema labarai a birnin Moscow cewa, gwamnatin Saudiyya tana yin amfani da karfi kan fararen hula marassa kariya da suke neman hakkokinsu da aka haramta musu, wanda hakan yay i hannun riga da abin da gwamnatin Saudiyya take raya na neman kare hakkokin bil adama a Syria.
Tun bayan kama babban malamin yankin Awamiyya na gabacin kasar Saudiya a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, yankunan gabacin kasar ke ci gaba da fuskantar boren al’umma, wanda dubban jami’an tsaro ke ci gaba da yin amfani da karfi domin murkushe masu boren. 1051692