IQNA

Fadakar Musulmi Na Da Dangantaka Da Juyin Juya Halin Musulunci

18:01 - July 14, 2012
Lambar Labari: 2368182
Bangaren kasa da kasa, fadakar da musulmi da larabawa suka yi a cikin lokutan nan na da dangantaka ne kai tsaye da juyin juya halin muslunci wanda ya zama digon dan ban a farkar da musulmin duniya domin dawo da karamarsu da kuma kare yanci da yan adamtaka.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar latabijin din press TV fadakar da musulmi da larabawa suka yi a cikin lokutan nan na da dangantaka ne kai tsaye da juyin juya halin muslunci wanda ya zama digon dan ban a farkar da musulmin duniya domin dawo da karamarsu da kuma kare yanci da yan adamtaka bisa koyarwa ta addini.
Babban jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar kasashen yammaci ba su fahimci cewa ta hanyar sanya wa Iran takunkumi suna kara wa al'ummar kasar karfin gwuiwa ne wajen fada da duk wata barazana a kansu kamar yadda suka yi shekaru talatin da wani abin da suka wuce ba.
Jagoran ya bayyana hakan ne a lokacin ganawarsa da mahalarta taro na farko na kasa da kasa kan mata da farkawa ta Musulunci da ke faruwa da aka gudanar a Tehran inda ya ce tsaron shekaru talatin din da suka gabata al'ummar Iran sun tsaya kyam wajen fuskantar duk wani takuri daga makiya ta hanyar sadaukar rayuwarsu da dukiyoyin da ababen kaunarsu, wanda hakan ne ya sanya a halin yanzu Iran ta zamanto mai karfi sama da yadda take a da.
Yayin da ya koma kan rawar da mata suke takawa wajen ciyar da al'umma gaba da kuma farkar da al'umma, Jagoran ya ce rawar da suke takawa din rawa ce mai muhimmanci yana mai cewa duk wani yunkurin neman sauyi da mata suka shigo cikinsa to kuwa zai yi nasara.

1051602

captcha