IQNA

Za A Bude Bankin Musulunci A Kasar Mauritania Nan Ba Da Jimawa Ba

18:01 - July 14, 2012
Lambar Labari: 2368183
Bangaren kasa da kasa, ministan kula da harkokin kudi a kasar Mauritania ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a bude reshen babban bankin muslunci a kasar domin amfanin ‘yan kasuwa da sauran mutane masu bukatar saka hannayen jari na cikin gida.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, ministan kula da harkokin kudi a kasar Mauritania ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a bude reshen babban bankin muslunci a kasar domin amfanin ‘yan kasuwa da sauran mutane masu bukatar saka hannayen jari na cikin gida dama yan kasar da suke ketare.
Shi kuwa shugaban kasar Sudan Umar Hasan Albashir ya isa kasar Habasha domin halattan zaman taron kungiyar tarayyar Afirika.
Rahotonni sun bayyana cewar shugaban kasar Sudan Umar Hasan Albashir ya isa birnin Addis Ababa fadar mulkin kasar Habasha domin halattan zaman taron kungiyra tarayyar Afirika da za a fara gudanarwa a ranar lahadi mai zuwa.
Wakilin kasar Sudan a kungiyar tarayyar Afirika Abdurraham Sar-Khatam ya bayyana cewa shugaban kasar na Sudan zai gudanar da zaman tattaunawa da fira ministan kasar ta Habasha Males Zinawi dangane da shiga tsakani da kasar ta Habasha ke yi a rikicin kasar Sudan da makobciyarta Sudan ta Kudu.
A baya an shirya gudanar da zaman taron kungiyar ta tarayyar Afirika ne a kasar Malawi amma aka dage zuwa kasar Habasha sakamakon alwashin da gwamnatin Malawi ta yi na kame shugaban kasar Sudan Umar Hasan Albashir matukar ya shiga cikin kasarta domin mika shi ga kotun kasa da kasa da ke hukunta manyan laifuka a duniya da ke nemansa ruwa ajallo.
1051589





captcha