IQNA

Ana Nuna Ma MaTa Musulmi Masu Hijabi Wariya A Kasar Faransa

13:36 - July 16, 2012
Lambar Labari: 2369907
Bangaren kasa da kasa, ana ci gaba da nuna ma mabiya addinin Musulunci na kasar Faransa wariya da suke saka hijabi tare da kyamarsu a cikin lamurra da dama da suka danganci gwamnati wuraren karatu musamman kamar dai yadda rahotonni suka tabbatar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, ana ci gaba da nuna ma mabiya addinin Musulunci na kasar Faransa wariya da suke saka hijabi tare da kyamarsu a cikin lamurra da dama da suka danganci gwamnati wuraren karatu musamman kamar dai yadda rahotonni suka tabbatar.
A jiya ne sakatariyar harkokin wajen kasar Amurka H. Clinton ta gana da shugaban kasar Masar Muhammad Mursi a ziyarar aiki da take gudanarwa a kasar ta Masar, wadda irinta ce ta farko da ta kai kasar tun bayan zaben Mursi a matsayin sabon shugaban kasar a cikin watan Yunin da ya gabata.
Jim kadan bayan ganawar da ta gudana tsakaninta da sabon shugaban kasar ta Masar, H. Clinton ta gudanar da taron amnema labarai tare da takwaranta na kasar Masar Muhammad Amru, inda ta bayyana cewa ganawarta da Muhammad Mursi ta yi armashi matuka, ta ce manufar ziyarar tata dai ita ce nuna cikakken goyon bayan Amurka ga tsarin demokradiyya a kasar Masar, wadda ta kasance sakamako ne na sadukantarwar da al'ummar kasar suka yi.
Wani babban jami'i a ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ya fadi cewa daga cikin muhimamn abubuwan da Clinton take zantawa da jami'an kasar Masar kansu, akwai batun yarjejeniyar zaman lafiya da haramtacciyar kasar Isra'ila, wadda Masar ita ce kasa ta farko a cikin kasashen larabawa da fara rattaba hannu kan irin wannan yarjeneiya tare da gwamnatin yahudawan Sahyuniya a cikin shekara ta 1979, a lokacin mulkin Anwar Sadat, wanda hakan ya fuskanci kakkausar suka daga a'ummar Masar da ma sauran al'ummomin larabawa da na musulmi a duniya, kuma har inda yau take.
1052922












captcha