Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an bayyana sunayen wasu daga cikin mutanen da suka karbi addinin muslunci a cikin wannan shekara a wajen taron baje kolin kur'ani mai tsarki wanda shi ne karo na farko da ake nuna hakan a irin wannan taro kasantuwar lamarin yana da matukar tasiri wajen kara karfafa gwiwar musulmi kan bin tafarkin addinin mai tsarki kamar yadda Allah madaukakin sarki ya yi umurni.
A lokacin da yake gabatar da jawabinsa awajen bude taron baje kolin,
shugaban kasar Iran Dakta Mahmoud Ahmadinejad ya ce har abada mafarkin da kasashe makiya jamhuriyar musulunci ta Iran ke yi na ganin cewa sun durkusar da kasar ta hanyar takunkumai da wasu hanyoyi na takurawa ba zai taba kai ga samun nasara ba.
Ahmadinejad ya bayyana hakan ne a yau lokacin da yake kaddamar da wata masana'antar kera jiragen kasa a garin Karaj da ke wajen birnin Tehran, yana mai cewa a tsawon shekaru 33 da samun nasarar kafa tsarin musulunci a kasar, ba wata illar da makircin wadannan kasashe ya haifar wa Iran face ci gaba da kuma cusa wa al'ummar kasar ra'ayin dogoro da kai wajen kirkire da kuma kafa masana'antu.
Shugaban na Iran ya ce ko shakka babu kwararri da kuma sauran injiniyoyi na kasar sun taka gagarumar rawa wajen gina kasar da kuma tattalin arzikinta, inda a sakamakon hakan takunkumai da kuma hanyoyi na takurawa da kasashen Turai da Amurka ke amfani da su ba su yi wani tasiri a kan kasar da kuma ci gabanta ba.
1055947