IQNA

Madaba’antar Beirut Ta Halarci Taron Baje Kolin Kur’ani Da Ake Gudanarwa

13:57 - July 19, 2012
Lambar Labari: 2372527
Bangaren kasa da kasa, babbar madaba’antar birnin Beirut a kasar Lebanon ta halarci taron baje kli da ake gudanarwa yanzu a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar muslunci ta Iran karo na ashirin tare da fitar da muhimman abubuwa da suka danganci kur’ani mai tsarki kamar dai yadda aka saba gudanarwa a kowace shekara.
Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, babbar madaba’antar birnin Beirut a kasar Lebanon ta halarci taron baje kli da ake gudanarwa yanzu a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar muslunci ta Iran karo na ashirin tare da fitar da muhimman abubuwa da suka danganci kur’ani mai tsarki kamar dai yadda aka saba gudanarwa a kowace shekaraa wannan wuri.
A wani labarin na daban kuma jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da kashe ministan tsaron kasar Siriya tare da mika ta'aziyyarta ga gwamnati Siriya da al'ummar kasar.
Shugaban bangaren kula da kasashen Larabawa da Afirika a ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Husain Amir Abdul-Ilahiyon ya yi tofin Allah tsine kan harin ta'addancin da aka kai birnin Damasqas fadar mulkin kasar Siriya a jiya laraba, harin da ya yi sanadiyar mutuwar manyan jami'an tsaron kasar ciki har da ministan tsaron Siriya.
Amir Abdul-Ilahiyon ya kuma bayyana cewa; wadanda suke aikewa da makamai tare da goyon bayan ayyukan ta'addanci a kasar ta Siriya da yardan Allah ba zasu taba cimma nasara ba.
A gefe guda kuma ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Akbar Salihi ya yi ta'aziyyar kashe ministan tsaron Siriya da sauran manyan jami'an kasar ga takwaransa na Siriya Walid Mu'allim.
Har ila yau mataimakin shugaban kasar Iran Muhammad Ridha Rahimi ya mika sakon ta'aziyya ga fira ministan kasar Siriya, tare da jaddada cewa wannan hare haren ta'addancin da ake kai wa kan kasar ba zai taba raunana gwamnatin Siriya kan yakin da take yi da ayyukan ta'addanci ba.
1056944


captcha