IQNA

Masallatan Kasar Indonesia Suna Bayar da Buda Baki Ga Masu Azumi

17:50 - July 21, 2012
Lambar Labari: 2373890
Bangaren siyasa da zamantakewa, masallatai a garuruwan kasar Indonesia suna bayar da buda baki ga masu azumi bayan sallar magriba kamar dai yadad hakan ya zama tsohuwar al’ada ce ga al’ummar kasa wadda ta ita ce tafi kowace kasa ta duniya yawan mabiya addinin muslunci.
Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa masallatai a garuruwan kasar Indonesia suna bayar da buda baki ga masu azumi bayan sallar magriba kamar dai yadad hakan ya zama tsohuwar al’ada ce ga al’ummar kasa wadda ta ita ce tafi kowace kasa ta duniya yawan mabiya addinin muslunci kamar dai yadda kididdiga ta tabbatar.
A bangare guda kuma a jiya ne sakatariyar harkokin wajen kasar Amurka H. Clinton ta gana da shugaban kasar Masar Muhammad Mursi a ziyarar aiki da take gudanarwa a kasar ta Masar, wadda irinta ce ta farko da ta kai kasar tun bayan zaben Mursi a matsayin sabon shugaban kasar a cikin watan Yunin da ya gabata.
Jim kadan bayan ganawar da ta gudana tsakaninta da sabon shugaban kasar ta Masar, H. Clinton ta gudanar da taron amnema labarai tare da takwaranta na kasar Masar Muhammad Amru, inda ta bayyana cewa ganawarta da Muhammad Mursi ta yi armashi matuka, ta ce manufar ziyarar tata dai ita ce nuna cikakken goyon bayan Amurka ga tsarin demokradiyya a kasar Masar, wadda ta kasance sakamako ne na sadukantarwar da al'ummar kasar suka yi.
Wani babban jami'i a ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ya fadi cewa daga cikin muhimamn abubuwan da Clinton take zantawa da jami'an kasar Masar kansu, akwai batun yarjejeniyar zaman lafiya da haramtacciyar kasar Isra'ila, wadda Masar ita ce kasa ta farko a cikin kasashen larabawa da fara rattaba hannu kan irin wannan yarjeneiya tare da gwamnatin yahudawan Sahyuniya a cikin shekara ta 1979, a lokacin mulkin Anwar Sadat, wanda hakan ya fuskanci kakkausar suka daga a'ummar Masar da ma sauran al'ummomin larabawa da na musulmi a duniya, kuma har inda yau take Masar na nan daram kan wannan yarjejeniya.
1057625


captcha