IQNA

Gasa Tana Karfafa Gwiwar Matasa Wajen Mayar Da Hankali Ga Kur’ani Mai Tsarki

11:55 - July 22, 2012
Lambar Labari: 2374440
Bangaren kasa da kasa, bisa la’akari da muhimmancin da gasar karatun kur’ani mai tsarki da shi wajen karafaf gwiwar matasa domin mayr da hankali kan kur’ani ya kamata kasashen musulmi su dauki matakai na samar da shiri zai taimaka wajen karfafa wannan bangare a cikin kasashensu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna yab habarta cewa yta nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa cewa, a zantawar da ta hada shi da wakiili Sudan a gasar Kur’ani Isma’il Dahiyya ya sheda cewa bisa la’akari da muhimmancin da gasar karatun kur’ani mai tsarki da shi wajen karafaf gwiwar matasa domin mayr da hankali kan kur’ani ya kamata kasashen musulmi su dauki matakai na samar da shiri zai taimaka wajen karfafa wannan bangare a cikin kasashensu, musamman a lokutan azumin watan Ramadan mai alfarma.
A wani labarin na daban kuma Sudan ta kudu ta sanar da dakatar da tattaunawa ta kai tsaye da take yi da makwabciyarta kasar Sudan sakamakon zargin da ta yi na cewa dakarun Sudan din sun kai mata hari ta sama lamarin da kasar Sudan din ta musanta.

Yayin da ya ke sanar da wannan matsaya da kasar Sudan ta Kudun ta dauka, kakakin tawagar Sudan ta Kudu a tattaunawar da kasashen biyu suka yi a birnin Adis Ababa a kwanakin baya Atif Kiir ya ce babu wani abin da ya rage wa Sudan ta kudun in banda dakatar da wannan tattaunawar ta kai tsaye.

Ita kuma a nata bangaren kasar Sudan, ta bakin mai magana da yawun sojin kasar Al-Sawarmi Khalid, ta musanta wannan zargin da makwabciyartan ta yi mata na kai harin soji ta sama yankin Rumaker dake arewacin tekun Nahr al-Ghazal.

A yau lahadi ne dai ake sa ran kasashen biyu za su sake komawa teburin tattaunawar a helkwatar kungiyar Tarayyar Afirka da ke birnin Adis Ababa na kasar Ethiopia mako guda bayan da shugabannin kasashen biyu Umar Hasan al-Bashir da Silva Kiir suka gudanar da ganawarsu ta farko don magance matsalolin da suka kunno kai tsakanin kasashen biyu.

1055728
captcha