IQNA

Sarkin Saudiyya Ya Yi Kira Da A Gudanar Da Zaman Gaggawa Na Kasashen Musulmi

13:31 - July 23, 2012
Lambar Labari: 2375527
Bangaren kasa da kasa, a daidai lokacin da al’ummomin larabawa suke bore a wasu kasashe gwamnatin wahabiyawan saudiyya ta kirayi wani zama da ta kira gaggawa na kasashen muuslmi a cikin wata mai domin tattauna muhimman batutuwa da suka addabi duniyar musulmi wanda amasana suke ganin cewa yunkuri ne na samun goyon bayan musulmi domin kara matsa lamba kan Syria.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, yanzu haka a daidai lokacin da al’ummomin larabawa suke bore a wasu kasashe gwamnatin wahabiyawan saudiyya ta kirayi wani zama da ta kira gaggawa na kasashen muuslmi a cikin wata mai domin tattauna muhimman batutuwa da suka addabi duniyar musulmi wanda amasana suke ganin cewa yunkuri ne na samun goyon bayan musulmi domin kara matsa lamba kan Syria wada ta zama karfen kafa wajen hana aiwatar da siyasar turai a yankin.
A wani labarin na daban kuma sojojin Siriya sun kashe 'yan tawayen kasar fiye da 150 a samamen da suke kai wa da nufin tsarkake yankunan kasar daga masu dauke da makamai da suke samun tallafi daga kasashen yammaci da na Larabawa, rahotonni daga Siriya sun tabbatar da kashe 'yan tawaye fiye da 40 a yankin Basatinil- Mazah da ke birnin Damasqas fadar mulkin kasar, kuma dauki ba dadi tsakanin sojojin na Siriya da 'yan tawayen a yankin Ajjusiyya da ke kusa da kan iyaka da kasar Labanon ya lashe rayukan 'yan tawaye fiye da dari daya.
A yankin Qabtan-Ajjabal da ke arewacin garin Halab; sojojin gwamnatin Siriya sun halaka 'yan tawaye da dama ciki har da kwamandar masu dauke da makamai a yankin Mahmud Asshqar.
Har ila yau rundunar sojin Siriya ta fatattaki 'yan tawayen kasar daga kan iyakar kasarta da Iraki tare da girke jami'an tsaron gwamnatin Siriya a yankunan.
A gefe guda kuma kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya watsa labarin cewa: akwai 'yan tawayen Siriya kimanin dari da hamsin da suka hada da 'yan kasashen Larabawa da suka ja daga a kan iyakar Siriya da Turkiyya.
1059551

captcha