IQNA

An Nada Malami Mai Bayar Da Fatawa A Kasar Kyrgystan A Matsayin Rikon Kwarya

15:22 - July 23, 2012
Lambar Labari: 2375685
Bangaren siyasa, an malamai mai bayar da fatawa na wucin gadi a kasar Kyrgystan wnda zai rika kula da harkokin addini tare da amsa tambayoyin mutane da suka shafi lamurran fikihu da sauransu daga nan har zuwa lokacin da za a nada tabbataccen malami a nan gaba.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa na nahiyar Asia cewa, yanzu haka dai an malamai mai bayar da fatawa na wucin gadi a kasar Kyrgystan wnda zai rika kula da harkokin addini tare da amsa tambayoyin mutane da suka shafi lamurran fikihu da sauransu daga nan har zuwa lokacin da za a nada tabbataccen malami a nan gaba kamar dai yadda majiyoyin gwamnatin kasar suka tabbatar.
A nasa bangaren jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewar ci gaban al'ummar musulmi da wayewarsu sun samo asali ne daga koyarwar alkur'ani da kyawawan dabi'un Musulunci, a jawabin da ya gabatar a gaban taron makaranta da mahaddata da kuma malamai a fannin ilimin alkur'ani mai girma da suka ziyarce shi a yau asabar; Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullahi Uzma Sayyid Ali Khamene'i ya jaddada cewar shaharar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi ya samo asali ne daga dogaronta da Allah karkashin koyarwar alkur'ani mai girma; sannan yayi nuni kan sakamakon da mutum zai samu idan ya dogara da wayewa irin ta kasashen yammaci da ta ginu akan kawar duniya da nisantar kyawawan dabi'u yana mai jaddada cewa; babban misali kan da'awar karya da kasashen yammaci ke yi dangane da kare hakkin bil-Adama shi ne yin shiru kan kisan gillar da ake yi wa dubban musulmai a kasar Myanmar.
Jagoran ya kuma kara da cewa; wayewar yammaci tun a tsawon daruruwan shekaru da suka gabata har ya zuwa yanzu duk inda suka sanya kafa babu abin da zai bulla sai barna da bautar da dan Adam ta hanyar tatsarsa, don haka Jagoran juyin juya halin Musulunci ya fayyace cewar ta hanyar aiki da koyarwar alkur'ani ne kadai za a kai ga samun daukaka, amincin rayuwa, jin dadi na zahiri da badini, kyawawan dabi'u da samun nasara kan makiya.
1059002


captcha