IQNA

Taron Fadakarwa da Zai Yi Dubi Kan Mahangar Addinan Buda Da Musulunci

15:22 - July 23, 2012
Lambar Labari: 2375687
Bangaren siyasa da zamantakewa, wakilin jagoran juyin juya halin muslunci a kan lamurran hajji ya bayyana cewa ya zama wajibi a gudanar da taruka da zasu taimaka wajen kusanto da fahimta tsakanin mabiya addinan Musulunci da kuma buda domin samun fahimta tsakanin dukkanin bangarorin.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, wakilin jagoran juyin juya halin muslunci a kan lamurran hajji ya bayyana cewa ya zama wajibi a gudanar da taruka da zasu taimaka wajen kusanto da fahimta tsakanin mabiya addinan Musulunci da kuma buda domin samun fahimta tsakanin dukkanin bangarorin masu dadddiyar alaka da tarihi da zaman lafiya da fahimtar juna atsakaninsu.
Wani rahoton na daban kuma da dumi-duminsa ya tababtar da cewa hare haren ta'addanci sun lashe rayukan mutane fiye da 20 a kasar Iraki a jiya lahadi majiyar tsaron kasar Iraki ta sanar da cewa: Hare haren ta'addanci ta hanyar tada bama bamai a garuruwan Bagadaza, Mada'in, Ramadi da Najaf sun lashe rayukan mutane fiye da 20 tare da jikkata wasu da dama.
Majiyar ta kara da cewar mafi muni daga hare haren da aka kai a jiyan shi ne na yankin Mahmudiyya da ke birnin Bagadaza fadar mulkin kasar ta Iraki, inda a akalla mutanen da suka rasa rayukansu suka haura goma, kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya bayyana cewar yawan mutanen da suka jikkata sakamakon hare haren na jiya sun doshi dari daya.
Malamin kuma wakilin jagoran juyin juya halin muslunci a kan lamurran hajji ya bayyana cewa ya zama wajibi a gudanar da taruka da zasu taimaka wajen kusanto da fahimta tsakanin mabiya addinan Musulunci da kuma buda domin samun fahimta tsakanin dukkanin bangarorin masu dadddiyar alaka da tarihi da zaman lafiya da fahimtar juna atsakaninsu da ake kokarin bata wannan alaka yanzu.
1059384

captcha