Kmafanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na taron baje kolin kur’ani cewa, yanzu haka cibiyar da ke kula da harkokin da suka danganci gwagwarmayar al’ummomin Lebanon da palastinu ta fitar da wani samfuri na masallacin Qods mai alfarma wanda aka tsara shi da shii nan aura mai kwakwalwa kuma aka saka bayanai na jagoran juyin juya halin muslunci a cikin da kuma bayanai na shugaban kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah, dangane da batutuwa da suka shafi gawgwarmaya da yahudawan sahyuniya.
A wani bayanin kuma na daban, za'a gudanar da zanga zanga a gaban ofishin majalisar dinkin duniya da ke nan birnin Tehran a ranar gobe talata don nuna goyon baya ga musulman kabilar Rohinga na kasar Myanmar wadanda gwamnatin kasar ke jagorantar shafesu daga kasar, a wani bayani wanda wata kungiya mai suna "International Action Group" ya rabawa yan jaridu a yau litinin, kungiyar ta yi kira ga kasashen duniya da su tsawatawa gwamnatin kasar Myanmar ta kawo karshen kisan musulmai kabilar Rohinga da take yi.
A bisa wasu bayanai wanda gungun wasu kungiya masu zaman kansu a kasar Britania suka fitar, sun ce daga ranar na watan yunin da ya gabata akalla musulmi yan kabilar Rohinga ne aka kashe a kasar Myanmar, sannan wasu kuma suka bace, a yayinda wasu akalla dubu 80 kuma suka kauracewa gidajensu sanadiyyar tashe tashen hankula wanda gwamnatin kasar take jagoranta.
Tun fiye da shekaru biyu da suka gabata ne musulmi yan kabilar Rohinga na kasar Myanmar a yankin kudu maso gabacin Asia suka fara tserewa daga kasarsu sanadiyyar tsongama daga hukumamin kasar.
Gwamnatin kasar ta Myanmar dai a fili ta bayyanawa duniya cewa yan kabilar Rohinga ba yan kasar ba ne duk da cewa iyayensu sun rayu karnuka masu yawa a kasar, wanda bisa dokoki na kasa da kasa babu dalilin bayyanasu a matsayin mutanen da ba ‘yan kasa ba.
1060750