IQNA

Tsohon Jakadan Iran A Birtaniya Ya Halarci Taron Baje Kolin Kur'ani Mai Tsarki

11:06 - July 25, 2012
Lambar Labari: 2377069
Bangaren kasa da kasa, tsohon jakadan jamhuriyar muslunci ta Iran ya halarci taron baje kolin kur;'ani mai tsarki da ake gudanarwa a birnin Tehran domin gane wa idanunsa irin abubuwan da aka baje wurin da suke da dangantaka da kur'ani da kuma kayyaykin muslunci kamar dai yadda aka saba gudanar kimanin shekaru ashirin da suka gabata.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a lokacin da yake halartar taron na baje kolin kur'ani a birnin Tehran, tsohon jakadan jamhuriyr muslunci ta Iran a Birtaniya ya bayyana cewa, kyawawan dabiu a matsayin bababn abin da ke yin tasiri fiye da komai wajen isar dasakon addini ga sauran mutane domin kuwa hakan yana da cikin cikin hanyoyi na hikima da wa'azi kyakywa wanda aka umurci manzon Allah tsira da amincin su tabbata a gare shi da ya yi kira ta hanyar yin amfani da su a lokacin yake yin kira zuwa ga addinin madaukakin sarki a Makka da kuma rayuwarsa baki daya bayan hijira.

Hassan Faghih tsohon jakadan ya kara da cewa, a lokacin mai isar da sako ya lizimci aikata a bin da Allah ya umurce da kuma kaurace ma duk abin da Allah ya yi hani ya kyautata dabiu da halayyarsa acikin mutane, to ko shkaka babu abin da yake nufin iusar musu das hi zai ggarumin tasiri, domin kuwa a lokacin da mutum yake kira zuwa ga wani abu to aga bin da yake kira a cikin aikinsa, maimakon fadar hakan kawai a fatar baki ba btare da iki ba.

Tsohon jakadan jamhuriyar muslunci ta Iran ya halarci taron baje kolin kur;'ani mai tsarki da ake gudanarwa a birnin Tehran domin gane wa idanunsa irin abubuwan da aka baje wurin da suke da dangantaka da kur'ani da kuma kayyaykin muslunci kamar dai yadda aka saba gudanar kimanin shekaru ashirin da suka gabata duk kuwa da cewa taron ya kara samun gagarumin ci gaba.

1061654


captcha