Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Daily Times, cewa an bude wani taron baje koli na kyakyawan rubutun Musulunci a birnin Lahour na kasar Pakistan tare da halartar wakilan cibiyoyin addini da kuma madaba’antu na kasar da suke gudanar da ayyuka na buga littafai da kuma rubuce-rubucen addini da nufin kara fitoda matsayin addini da kuma gudunmawar da yake bayarwa a bangaren aladu da fasaha.
Wani rahoton kuma ya habarta cewa jJirgin sama maras matuki da Amurka ke amfani da shi domin kashe fararen hula, a safiyar yau ya kashe mutane akalla 10 a cikin yankunan kabilu da ke kusa da iyakar Afghanistan da kuma Pakkistan bisa zargin cewa wai su 'yan ta'adda ne.
Rahotanni sun ce jirgin ya harba makamai masu linzame akalla 6 a kan gidajen jama'a da ke kauyen Dray Nashtar na lardin Miranshah da ke cikin kasar Pakistan, inda kuma kamar yadda ta saba, hukumar leken asiri ta amurka wacce ke amfani da wadannan jirage ta ce wadanda ta kashen dukkaninsu 'yan ta'adda ne, alhali kuwa mazauna kauyen sun ce mutanen ba su da wata alaka da ayyukan tsageranci.
A can baya dai alkalumma sun yi nuni da cewa dubban mutane da ke rasa rayukansu sakamakon wadannan hare-hare na jiragen maras matuka, fararen hula ne amma ba 'yan ta'adda ba kamar yadda Amurkar ke ikirari.
1061301