Bangaren siyasa, mabiya addinin musluncida ke kasar Myanmar sun zama daga cikin al’ummomin da suka fi zama masu fuskantar zalunci da danniya da wariya daga mabiya addinin buda da kuma mahukuntan kasar da suke kokarin mayar da su saniyar ware da tabbatar da cewa sub a yan kasa ne ba.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, masana suna bayyana cewa mabiya addinin musluncida ke kasar Myanmar sun zama daga cikin al’ummomin da suka fi zama masu fuskantar zalunci da danniya da wariya daga mabiya addinin buda da kuma mahukuntan kasar da suke kokarin mayar da su saniyar ware da tabbatar da cewa sub a yan kasa ne ba wanda hakan ya zama dalilin kashe su da kone su.
A nasu bangaren malaman addinin Musulunci a Cibiyar ilimi ta Azhar da ke kasar Masar sun bukaci aikewa da taimakon jin kai ga musulman kasar Myanmar wato Bama da suke fuskantar bakar siyasar zalunci, A bayanin da malaman cibiyar ilimin ta Al-Azhar da ke kasar Masar suka fitar a yau laraba sun jaddada yin Allah wadai da kisan kiyashin da ake yi ga al'ummar musulmin Myanmar da hadin bakin jami'an tsaron kasar, tare da yin kira ga kungiyoyin Musulunci musamman kungiyar hadin kan kasashen musulmi da su dauki matakin hanzarta aikewa da taimakon gaggawa ga musulmin kasar ta Myanmar.
A birnin Tehran na kasar Iran ma an gudanar da zanga zangar yin Allah wadai da kisan kiyashin da ake yi wa musulmai a kasar ta Myanmar tare da neman kawo karshen wannan aiki na ta'addanci, Al'ummar musulmi sune mafiya karanci a tsakanin mabiya addinai a kasar Myanmar don haka gwamnatin kasar ke daukansu a matsayin baki da ba su da cikekken hakkokin 'yan kasa.
1061875