Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa dangin imam Musa Sadr sun karyata labaran da ake yayatawa kan makomar Imam Musa Sadr da abokan tafiyarsa a kafofin yada labarai musamman ma na kasashen larabawa da suke aiwatar da bakar siyasar Amurka da yahudawan sahyuniya a kan sauran al’ummomin larabawan yankin gaban ta tsakiya.
A nasa bangaren shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Birri ya sheda cewar, daya daga muhimmanabubuwa da gwamnatin kasar Lebanon ta mayar da hankali kansu a halin shi ne sanin makomar Imam Musa Sadr a kasar Libya bayan da marigayi kanar Gaddafi ya sace shi tare da abokan tafiyarsa su biyu tun sama da shekaru talatin da hudu da suka gabata.
A bangare guda kuma ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar kasar Lebanon ta Al-intiqad cewa, kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon ta yi kakausar suka tare da yin Allawadai da halartar wasu daga cikin kasashen larabawa taron da haramtacciyar kasar Isra’ila za ta gudanar mai taken tsaron yahudawan sahyuniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa ko shakka babu irin mika wuya da wasu daga cikin larabawa ke yi kai tsaye ga manufofin yahudawan sahyuniya, ya kara tabbatar da cewa dukkanin abin da haramtacciyar kasar Isra’ila take na cin zarafin al’ummar palastinu da sauran larabawa akwai hadin baki tsakaninta da wasu daga mayaudaran gwamnatocin larabawa.
Kungiyar ta hizbullah a kasar Lebanon ba ya ga kakausar suka tare da yin Allawadai da halartar wasu daga cikin kasashen larabawa taron da haramtacciyar kasar Isra’ila za ta gudanar.
1061977