IQNA

Sanar Da Shafin Yanar Gizo Na Kur’ani A Cikin Harshen China A Baje Kolin Kur’ani

12:10 - July 28, 2012
Lambar Labari: 2378904
Bangaren kasa da kasa, bangaren da ke kula da harkoki na ala’du da ilimi a taron baje koli na duniya ya sanar da wani sabon shafin yanar gizo na kur’ani mai tsarki a cikin harshen kasar China wanda ya kunshi tarjama ta kur’ani da tafsirai da sauran abubuwa da suka danganci kur’ani da aka tarjama a cikin wannan harshe.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya ahbarat cewa ya nakalto daga bangaen watsa labaransa, cewa bangaren da ke kula da harkoki na ala’du da ilimi a taron baje koli na duniya ya sanar da wani sabon shafin yanar gizo na kur’ani mai tsarki a cikin harshen kasar China wanda ya kunshi tarjama ta kur’ani da tafsirai da sauran abubuwa da suka danganci kur’ani da aka tarjama a cikin wannan harshe wanda ya zama daya cikin muhimman harsunan duniya.
Kasar Iran ba zata canza matsayinta ba tare da duk irin takura mata da kasashen yamma suke yi. Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar Iran Aya. Sayyeed Aliyul Khaminaee ne ya bayyana haka a jiya talata a lokacin da yake ganawa da jami'an gwamnatin kasar a gidansa a nan Tehran, jagoran ya kara da cewa, takunkumin tattalin arziki wanda kasashen yamma tare da jagorancin kasar Amurka suka dorawa kasar ba zai taba durkusadda gwamnatin kasar Iran zuwa ga bukatun wadannan kasashe ba.

Sun fake da shirin nuclear kasar Iran da kuma kare hakkin bil'adama a kasar, amma babbar manufarsu ita ce ganin bayan tsarin Musulunci wanda yake jagorancin kasar tun fiye da shekaru 30 da suka gabata, tsarin da ya ce yana samun goyon bayan alummar kasar, muna ganin irin matsalolin da suma wadannan kasashen suke fama da su, da kuma irin koma bayan da musamman kasar Amurka suka fuskanta a kasashen Afganistan Iraqi da kuma sauran kasashen duniya, ya kara da cewa, matsalolin tattalin arzikin da kasahen turai da kuma Amurkan kanta suka fuskanta a halin yanzu yana dada nuna mana cewa nasara tana gaba da yardar Allah.

1063587






captcha