Kamfanin diallcnin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa matasan shi’a da sunna sun mike tsaye domin shiga kafar daya da mabiya tafarkin akidar wahabiyanci da suke kafirta sauran musulmi suna ganin kowa kafiri ne bia ga mummanr akidar da aka dora su kanta wadda take bata sunan sunan addinin muslunci a idon duniya kamar yadda kowa ya sheda.
asana kan harkokin soji sun yi imanin cewa, ko shakka babu yanayin yadda aka kai hari kan babban ginin majalisar tsaron kasar Syria a ranar Laraba da ta gabata, da kuma irin bama-baman da aka yi amfani das u wajen kai harin, na tabbatar da cewa akwai hannun wasu manyan kasashen duniya, kuma manufar hakan ita ce karya zuciyar sojojin kasar domin su balle, to amma sai tsafi ya juya kan boka, domin kuwa hakan ya zaburar da sojojin kasar fiye da kowane lokaci .
Tun da aka kunna wutar rikicin, wajen ganin cewa sun kawo karshen 'yan ta'adda a kasar, bababn dalili kan hakan kuwa shi ne yadda su kansu kasashen turai da suke daukar nauyin 'yan ta'addan suka yarda cewa yaran nasu kam a halin yanzu suna yaba wa aya zaki a hannun dakaron Syria, dalili na biyu kuma shi ne yadda a jiya Lahadi 'yan ta'adda na Syria suka yi kira ga dakarun gwamnati da a dakatar da bude wuta na wani dan lokaci, kiran da rundunar sojin ta yi watsi da shi, tare da tabbatar da cewa abin da suke yi yaki ne tsakaninsu da Amurka da Isra'ila, da babu ja da baya a kansa.
1066908