IQNA

An Yi Kira Da A Bayar Da Muhimmanci Ga Sahihin Alkalanci A lokacin Gasar Kur'ani

9:52 - August 04, 2012
Lambar Labari: 2384657
Bangaren kasa da kasa, an yi kira da a bayar da muhimmanci ga alkalancin gasar kur'ani mai tsarki ta daliban jami'a na kasashen musulmi musamman kan batun sauti da kuma yadda hakan yakan yi tasiri wajen samun maki a tsakanin alakalan gasar wadanda suka fito daga kasashe duniya.

Kamfanin dillancin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga bangaren yada labaransa na cikin gida, cewa daya daga cikin alkalan gasar kur'ani ya yi kira da a bayar da muhimmanci ga alkalancin gasar kur'ani mai tsarki ta daliban jami'a na kasashen musulmi musamman kan batun sauti da kuma yadda hakan yakan yi tasiri wajen samun maki a tsakanin alakalan gasar wadanda suka fito daga kasashe duniya, musamman daga kasashen musulmi da na larabawa.

A wani labarin na daban kuma gwamnatin kasar Tunisiya ta gabatar wa Majalisar Dokokin kasar da wani daftarin doka da zai bayar da damar hukunta duk wanda aka sama da laifin wajen cin zarafin addinin musulunci da kuma sauran addinai saukakki daga Ubangiji. Shugaban kwamitin rubuta sabon kundin Tsarin mulki a Majalisar Dokokin ta kasar Tunisiya Habib Khedher ne ya tabbatar da cewa tuni wannan daftarin doka ya shiga hannun kwamintin da yake jagoranta.

Dokar dai za ta hukuntar da duk wanda aka sama da laifuka kan cin zarafi, wulakantarwa ko kuma furta wasu kalaman batanci ga Ubangiji da kuma Manzon Allah mai tsira da amincin Allah da iyalansu gidansa tsarkaka, da dukkanin annabawan Allah, da littafin Alkur'ani mai girama da kuma sauran littatafai saukakki daga Ubangiji, da masallatai, dan coci-coci da kuma kuma wuraren ibadar addinin Yahudanci.

Kasar Tunisia dai ta kasance kasa ta farko da ta fara fuskantar bore daga al'umma wada ya kai ga kifar da gwamnatin kama karya ta tsohon shugaban kasar Zainul abiding Bin Ali, wanda yanzu haka yake gudun hijira a kasar Saudiyya.

1068559



















captcha