Bangaren kasa da kasa, majalisar musulmin kasar Amurka ta bukaci da adauki dukaknin matakan da suka dace domin hana zubar da jinin musulmin kasar Myanmar babu gaira babu sabar wanda kasashen duniya suna ji suna gani ake yi wannan kisan gill aba tare da sun yi wani abin a zo a gani ba.
Kamfanin dilalcnin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CAIR, cewa majalisar musulmin kasar Amurka ta bukaci da adauki dukaknin matakan da suka dace domin hana zubar da jinin musulmin kasar Myanmar babu gaira babu sabar wanda kasashen duniya suna ji suna gani ake yi wannan kisan gill aba tare da sun yi wani abin a zo a gani ba domin samar da kwanciyar hankali a kasar.
A bangare guda kuma taron kasa da kasa da aka gudanar a kasar Malesiya ya yi Allah wadai da kisan kiyashin da ake yi wa al'ummar musulmi a kasar Myanmar wato "Bama". Taron kasa da kasa da aka gudanar a birnin Kuala Lumpur fadar mulkin kasar Malesiya a jiya juma'a ya bayyana kisan gillar da ake yi wa musulmai a kasar Myanmar musamman a jihar Rakhine da cewar take hakkin bil-Adama ne da ya yi hannun riga da dokokin kasa da kasa.
Mahalatta zaman taron sun kuma bukaci daukan matakin matsin lamba kan gwamnatin Myanmar domin ta bada izini ga kungiyoyin kasa da kasa musamman kungiyar hadin kan kasashen musulmi don su kai taimakon gaggawa ga musulmin da suke cikin muwuyacin hali. Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ce ta bukaci gudanar da zaman taron, kuma kungiyoyin kasa da kasa kimanin 30 ciki har da Majalisar Dinkin Duniya ne suka halacci taron
1070480