Bangaren kasa da kasa, makarancin kur’ani mai tsarki daga jamhuriyar muslnci ta Iran ya nuna rashin gamsuwa da yadda ake gudanar da alkalanci a gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki da ke gudana a birnin Dubai na kasar hadaddiyar daular larabawa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga safin sadarwa na yanar gizo, cewa makarancin kur’ani mai tsarki daga jamhuriyar muslnci ta Iran ya nuna rashin gamsuwa da yadda ake gudanar da alkalanci a gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki da ke gudana a birnin Dubai na kasar hadaddiyar daular larabawa bisa la’akari dahukuncin da suke yankewa, wanda ganinsa bai ginu kan alaci ba.
A wani labarin kuma jami’an tsaro a kasar Libya sun bayyana cewa wani bom wanda aka dana a wata mota ta tashi a kusa da wani ofishin yansanda a birnin Tripoli babban birnin Kasar. Majiyar yansandan ta kara da cewa wannan shi ne tashin bom na farko tun bayan faduwa gwamnatin tsohon shugaban kasar marigayi Muhammar Kazzafi. Tashin bom din dai ya dan raunata wani dan kasar Tunisia da ya ke kusa da wurin, babu wanda ya dauki nauyi ta da bom din sannan jami’an tsaro ma basu zargi da tashi shi.
An sha samun tashe tashen hankula a yankuna da dama a kasar Libya a cikin kwanakinnan, musamman a birnin Bengazi na gabacin kasar, amma rikici ne tsakanin kungiyoyi dauke da makamai ko kuma rikicin kabilanci. Har’ila yau a ranar tarlatan da ta gabata ce wasu mutanen dauke da makamai suka sace Iraniyawa 7 a birnin Bengazi. Iraniyawan masu bada agaji ne wadanda kuma suka je kasar ta Libya a bisa gayyatar kungiyar Red Cross na kasar , har yanzun dai ana kokarin ganin yan bindigan sun sake su.
1070863