Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa na cikin gida, shugaban taron baje kolin kur’ani mai tsarki na kasa da kasa ya gabatar da taron manema labarai domin bayyana abubuwan da suka gudana tun daga lokacin da aka fara taron na duniya inda ake bayyana muhimman ayyuka da aka gudanar da suka shafi kur’ani mai tsarki tun daga farkon watan ramadan mai alfarma tare da haartar masana da kuma walikan cibiyo.
A wani labarin na daban kuma babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah sayyid Hassan Nasrullah zai gabatar da jawabbi a yau dangae da abubuwan da suke faruwa yankin gabas ta tsakiya da kuma matsayin kungiyar a kansu musamman ma, wadanda suka danganci al’ummar larabawa da kuma haramtacciyar kasar Isra’ila.
Rahoton ya ci gaba da cewa a cikin jawabin nasa Sayyid Hassan Nasrullah zai mayar da hankali kan muhimman abubuwan da suke a gaban larabawa a halin yanzu, musamman a lokacin da shugabanninsu da sarakunansu suka zama manyan ‘yan kore ga manufofin haramtacciyar kasar Isra’ila da babbar uwar shaidanu Amurka.
Haka nan kuma zai yi tsokaci kan zaman taron koli na shugabannin larabawa da aka gudanar a birnin Bagadaza na kasar Iraki, tare da halartar wasu daga cikin shugabannin kasashen larabawa, yayin da larabawa tekun fasha suka kaurace ma zaman taron ba tare da bayyana wani dalili ba.
1076786