IQNA

Jami’an Tsaron Kasar Habasha Sun Kame Wani Dan jarida Musulmi

17:00 - August 13, 2012
Lambar Labari: 2392107
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaron kasar Habasha sun kame wani dan jarida musulmi bayan da ya watsa wani rahoto dangane da wani gangami da mutanen kasar suka yi domin nuna rashin amincewarsu da salon mulkin kasar da kuma neman sauyi da garambawul a cikin harkokin da ake tafiyar da mulkin kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daha shafin sadarwa na yaar gizo na rfi cewa, jami’an tsaron kasar Habasha sun kame wani dan jarida musulmi bayan da ya watsa wani rahoto dangane da wani gangami da mutanen kasar suka yi domin nuna rashin amincewarsu da salon mulkin kasar da kuma neman sauyi da garambawul a cikin harkokin da ake tafiyar da mulkin kasar.
Mahukuntan kasar Habsha dai sun kame wannan musulmi ne mai suna Yusuf Kashu dan jarida da ya yi rubutu kan yadda musulmin kasar suke nuna rashin gamsuwar da yadda ake cin zalunsu a kasar, da kuma yadda aka mayar da su saniyar ware a cikin dukaknin harkokin mulki da siyasa, kasantuwar cewa su ne marassa rinjaye idan aka kwatanta mabiya addinin kirista wadanda su en suke da rinjaye.
Bayanin ya kara da cewa jami’an tsaron kasar Habasha sun kame wani dan jarida musulmi bayan da ya watsa wani rahoto dangane da wani gangami da mutanen kasar suka yi domin nuna rashin amincewarsu da salon mulkin kasar da kuma neman sauyi da garambawul a cikin harkokin da ake tafiyar da mulkin kasar da ke gabacin nahiyar Afirka.
1076427


captcha