Bangaren kasa da kasa, an nuna wani kwafin kur’ani mai tsarki wanda shi ne mafi karanta a taron baje kolin kur’ani mai tsarki da ake gudanarwa abirnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar muslunci a karo na ashirin tare da halartar masana da kuma wakilan cibiyoyin addini.
Kmafanin dilalncin labaran iqna ya ahbarta cewa, ya nakalto daga shfain sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa a cikin gida cewa, a jiya an nuna wani kwafin kur’ani mai tsarki wanda shi ne mafi karanta a taron baje kolin kur’ani mai tsarki da ake gudanarwa abirnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar muslunci a karo na ashirin tare da halartar masana da kuma wakilan cibiyoyin addini musamman a bangaren ayyukan kur’ani.
Wani rahoton kuma na daban ya nuna cewa an gudanar da zaman taro matsayin Imam Amirul mumini (AS) a birnin Tantario na kasar Madagascar tare da lartar malaman addinin musuluci da kuma masana inda aka gudanar da bayani ga mahalrta taro tare da bayyana matsayinsa madaukaki bisa hujjoji da dalilai na nasii daga ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.
Ita kuwa kasar Afirka ta kudu ta maye gurbin haramtacciyar kasar Isra’ila da sunan palastinu a kan dukaknin kayyaykin da take fitarwa ko take shigo da su a cikin kasarta da hakan ya hada har da wadanda ake kawo daga harantacciyar kasar yahudawa maiimakon alamar su sai a saka ta palastinu a matsayin amintacciyar kasa.
Ana shirin gudanar da wani shiri da aka kira da yunkurin nuna goyon baya ga masallacin Qods ta hanayar sadarwa wanda hakan shi ne karon farko da masana a wannan bangaren za su gudanar da irin wannan shiri, kungiyar kasashen musulmi ta yi kakkausar suka da yin Allawadai da haramtacciyar kasar Isra’ila kan harin ta’addancin da ta kai masallatan musulmi palastinawa a cikin yankunan gabar yamma da kogin Jordan a cikin wannan mako.
1077618