Bangaren kasa da kasa, bababn burin al’ummar kasar Saliyo shi ne su bayar da kyautar wani daddden kur’ani mai tsarki ga jagoran juyin juya halin muslunci na Iran a matsayin abbabr kyauta kamar dai yadda shugaban bangaren yada labarai na ma’aikatar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakato daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa bababn burin al’ummar kasar Saliyo shi ne su bayar da kyautar wani daddden kur’ani mai tsarki ga jagoran juyin juya halin muslunci na Iran a matsayin abbabr kyauta kamar dai yadda shugaban bangaren yada labarai na ma’aikatar ya sanar a cikin wani bayani.
Jagoran 'yan adawa a kasar Chadi Saleh Kebzabo ya ce akwai bukatar gwamnatin kasar ta fito fili karara ta yi wa al'umma karin bayani a game da dalilanta na shirin aikewa da sojojin kasar domin yin aiki tare da sojojin kasashen yankin Yammacin Afirka da ake shirin turawa zuwa kasar Mali. Kebzabo ya ce ba wai yana adawa da aikewa da sojojin kasar domin taimaka wa wata kasa ta Afirka da ta fada a cikin matsaloli kamar Mali ba ne, to amma akwai bukatar gwamnati ta yi hakan a cikin haske da kuma samun yardar Majalisar Dokokin kasar, saboda a cewarsa sojojin Chadi ba mallakin shugaba Idris Debi ba ne.
A cikin kwanakin da suka gabata ne dai shugaban kasar ta Chadi Idris Deby Itno ya ce a shirye kasarsa take ta aike da sojoji zuwa Mali matukar dai Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shirin aikewa da runduna ta musamman da Kungiyar Ci gaban Tattalin Arzikin Kasashen Yankin Yammacin Afirka za ta yi a nan gaba.
1078991