Bangaren kasa da kasa, taron da shugabannin kasasen musulmi suka gudanar a birnin Makka na kasar Saudiyya ya yi kira da a kiyaye hakkokin musulmin kasar Myanmar da ake kashe su babu gaira babu sabar tare da daukar matakin korarsu daga kasar zuwa kasashe makwafta.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa taron da shugabannin kasasen musulmi suka gudanar a birnin Makka na kasar Saudiyya ya yi kira da a kiyaye hakkokin musulmin kasar Myanmar da ake kashe su babu gaira babu sabar tare da daukar matakin korarsu daga kasar zuwa kasashe makwafta kamar Bangaladash.
Bayaninya kara da cewa kisan da aka yi musulmin kasar Myanmar zai zama cikin muhimman abubuwan da za a tattauna su a gaban taron bababn zauren majalisar diniin duniya kamar dai yadda kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta sanar a cikin wani bayani da ta fitar a taron da ta gudanar da siyasa a birnin Makka a cikin wannan makobayan da kasashen yammacin turai suka bukaci mahukuntan Saudiyya da su kira zaman taron.
Ita kuwa kungiyar hamas da ke iko da yankin Gaza ta kirayi shugabannin kasashen msuulmi da suke gudanar da taruka abirnin Makka da su dauki matakan da suka dace kan batun ta’annutin haramtacciyar kasar Isra’ila da yahudawa masu tsatsauran ra’ayi kan masallacin Qods da kuma wurare masu alfarma da ke birnin na Qods alkiblar musulmi ta farko.
1079522