Bangaren kasa da kasa, babban jami’in kasar Masar da ke kula da mashigar Rafah ya bayyana cewa an bude wannan mashiga har tsawon kwanaki uku domin bayar da dama ga palastinawa da suke lakahea cikin kasar Masar domin su koma zuwa yankunansu da kecikin yankin zirin Gaza.
Kamfanbin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CPI, cewa Ayyub Abu Shi’ar babban jami’in kasar Masar da ke kula da mashigar Rafah ya bayyana cewa an bude wannan mashiga har tsawon kwanaki uku domin bayar da dama ga palastinawa da suke lakahea cikin kasar Masar domin su koma zuwa yankunansu da kecikin yankin zirin Gaza kamar dai yadda ya sheda manema labarai.
kafofin yada labarai na kasashen yammacin turai suna taka gagarumar rawa wajen karfafa gwiwar masu akidar cin zarafin musulmi da kuma keta alfarmar musulmi da addinin musulunci a duniya kamar dai yadda muke gani a duniya musamman ma a cikin nahiyar turai.
an watsa labarai masu karo da juna dangane da makomar majalisar ministocin kasar masar karkashin jagorancin fira minitsna Kamal Janzuri wanda masu tsaurin ra’yin kishin islama suke tuhumarsa da kasawa yayin da majalisar sojin kasar ba ta ba shi goyon bayn da yake bukata wajen gudanar da ayyukansa na tafiyar da mulki.
Mambobin majasar dokokin kasar Masar sun yi kira da a safke babban malamin kasar mai bayar da fatawa bayan ya yi tafiya zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila ba tare da izinin majalisa da kuma yin shawara da majalisar malaman addinin muslunci ta kasar ba lamarin da ake kallonsa a matsayin wani babban kure. 1079653