Bangaren kasa da kasa, gwamnatin Afirka ta kudu ta amince da haramta kayayyakin haramtacciyar kasar Isra’ila daga cikin kayyaykin da ake shigowa da su cikin kasar kamar dai yadda bayanin gwamnatin kasar ya tabbatar a cikin shirin da ke akwai na yin garambawul a kan harkokin cinikayya da sauran kasashe.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Safir news cewa, gwamnatin Afirka ta kudu ta amince da haramta kayayyakin haramtacciyar kasar Isra’ila daga cikin kayyaykin da ake shigowa da su cikin kasar kamar dai yadda bayanin gwamnatin kasar ya tabbatar a cikin shirin da ke akwai na yin garambawul a kan harkokin cinikayya da sauran kasashe na duniya.
Gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta shiga cikin jerin kasashen da suka haramta kayyakin haramtacciyar kasar Isra’ila kamar yadda wasu kasashe suka dauki irin wannan matakin tun da jimawa domin nuna rashin amincewarsu da zaluncin da take yi kan al’ummar palastinu marassa kariya kamar dai yadda yhaudawan sahyuniya suka shahara da hakan.
An shirya kara da za agabatar a gaban shari’a kan wasu yahudawan sahyuniya masu wulakanta kur’ani mai tsarki a cikin yankunan palastinawa da haramtacciyar kasar Isra’ila ta mamaye domin tabbatar musu da cewa musulmi ba za su amince da abin da uke yi ba na keta alfarma kur’ani da sauran ababe masu alfarma a cikin addinin muslunci.
A bangare guda kuma a ci gaba da mayar da martanin da malaman addinin muslunci gami da masana suke yi kan malamin gwamnatin Qatar Yusuf Kardawi, ministan mai kula da harkokin addinin muslunci a palastinu Muhmud Habbash ya bayyana cewa fatawar da Yusuf Kardawi ya bayar da ke hana sauran musulmi ziyartar masallacin Qods mai alfarma ta sabawa koyarwar alkur’ani mai tsarki.
1083679