Bangaren kasa da kasa, mai da kin Imam Musa Sadr ta bayyana cewa ba a shirye take ta karbi diyya a matsayin mataki na rufe batun mijinta ba wanda aka sacea akasar Libya tun shekaru sama da talatin da suka gabata a lokacin mulkin tsohon shugaban kama karya na kasar.
Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na mujallar Al-nashar, cewa mai da kin Imam Musa Sadr ta bayyana cewa ba a shirye take ta karbi diyya a matsayin mataki na rufe batun mijinta ba wanda aka sacea akasar Libya tun shekaru sama da talatin da suka gabata a lokacin mulkin tsohon shugaban kama karya na kasar mu’ammar Gaddafi.
Wani labarin kuma yan salafiyya a Libya na ci gaba da rusa kabarukan magabata da su ka taka rawa wajen kafuwar addinin musulunci a cikin kasar da kuma makwabtanta. Gungun mutanen dai sun isa kabarin Sheikh al-shi'ab al-dahmani ne da safiyar yau asabar inda su ka yi amfani da buldoza wajen rusa shi a yammacin birnin Tripoli. A ranar juma'ar da ta gabata ma dai 'yan salafiyyar sun rusa kabarin sheikh Abdussalam al-Asmar a garin Zentan wanda ya rayu a karni na 16 miladiyya.
Yan salafiyyar dai sun rika yin kabbarori a lokacin da su ke rusa kabarin shehin malamain da kuma jami'ar da ya gina tun a lokacin da ya ke a raye fiye da shekaru 500 da su ka gabata. Bugu da kari maharan sun yi kaca-kaca da dakin karatu wanda ya ke hade da jami'ar mai kunshe da littatafai masu kima ta ilimi da tarihi. Makarantar sheikh Asmar ce cibiyar haddar al'kur'ani mafi girma a cikin kasar Libya baki daya. Kuma a lokacin rayuwarsa ya rubuta littatafai masu kima na fikhu da tarbiyyar ruhi da su ka hada; alwasiyyatul-kubra da al-Anwarussaniyyah. Har ila yau, yan salafiyyar sun rusa kabarin sheikh Ahmad al-zaruq a garin Misratah da ke da nisan kilo mita 200 daga birnin Tripoli. Fada ya barke da marecen ranar alhamis tsakanin 'yan salafiyyar da mutanen gari a wasu yankuna domin hana su ci gaba da rusa kabarukan malaman addinin musulunci.
1084060