Bangaren kasa da kasa, an saka lada ta makudan kudade ga wanda ya iya kure daya daga cikin fitattun malaman addinin muslunci da ke bin tafarkin iyalan gidan manzon Allah tsira da mnaincin Allah su tabbata a gare shi da ke tona a sirin miyagun malamai da suka zuba guba cikin akidar Musulunci suka halakar da musulmi da dama.
Kamfanin ilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam cewa, wasu daga cikin wahabiyawan Saudiyya sun saka lada ta makudan kudade ga wanda ya iya kure daya daga cikin fitattun malaman addinin muslunci da ke bin tafarkin iyalan gidan manzon Allah tsira da mnaincin Allah su tabbata a gare shi da ke tona a sirin miyagun malamai da suka zuba guba cikin akidar Musulunci suka halakar da musulmi da dama musamman Dan Taimiyya daga cikinsu.
Babban malamin wato Ayatollah Sayyid kamal Haidari ya dauki tsawon lokaci yana gudanar da shiri na addini tare da fadakar da musulmi kan muhimman abubuwan da suka rataya a kansu, domin hakan y aba su damar bin sahihin tafarki na ubangiji wanda ya umurci manzonsa da ya bi ba tare da bin son ran wasu da bas u san addini ba, kuma suka nada kansu a matsayin malamai suna halakar da mutane, lamarin da ya bakanta ran wahabiyawa, kuma suke kokarin ganin bayansa ko ta wace hanya.
Malaman wahabiyawan sun saka lada ta makudan kudade da ya kai riyal miliyan daya ga wanda ya iya kure daya daga cikin fitattun malaman addinin muslunci da ke bin tafarkin iyalan gidan manzon Allah tsira da mnaincin Allah su tabbata a gare shi da ke tona a sirin miyagun malamai da suka zuba guba cikin akidar Musulunci suka halakar da musulmi da dam aba tare da musulmin sun farga ba.
1084880