IQNA

Kasashen Yan Ba Ruwanmu Na Goyon Bayan shirin Iran Na Makamashin Nukiliya

17:09 - August 28, 2012
Lambar Labari: 2400847
Bangaren siyasa, sama da shekaru 10 da suka gabata kasashe ammbobi a kungiyar kasashe yan ba ruwanmu sun nuna cikakaen goyon bayansu ga shirin Iran an makamashin nukiliya na zaman lafiya duk kuwa da matsin lambar da suke fuskanta daga wasu daga cikin manyan kasashen turai.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa sama da shekaru 10 da suka gabata kasashe ammbobi a kungiyar kasashe yan ba ruwanmu sun nuna cikakaen goyon bayansu ga shirin Iran an makamashin nukiliya na zaman lafiya duk kuwa da matsin lambar da suke fuskanta daga wasu daga cikin manyan kasashen turai da kuma haramtacciyar kasar Isra’ila.
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta karbi ragamar jagorancin kungiyar 'yan ba ruwanmu ta NAM a yau talata. A jawabin da ya gabatar a yayin bude zaman taron ministocin wajen kasashen kungiyar 'yan ba ruwanmu ta NAM a birnin Tehran na kasar Iran wakilin minsitan harkokin wajen kasar Masar Ramzi Izzuddin Ramzi ya jinjinawa kasar Iran kan gagarumin shirin da ta yi na karbar bakwancin zaman babban taron kungiyar 'yan ba ruwanmu ta NAM da tsara zaman taron ta hanyar da ta dace.
A ci gaba da jawabinsa ga mahalarta zaman taron na kungiyar 'yan ba ruwanmu ta NAM wakilin ministan harkokin wajen kasar ta Masar Ramzi Azzuddin ya mika ragamar jagorancin kungiyar ta 'yan ba ruwanmu ta NAM ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran, inda kasar ta Iran zata shugabanci kungiyar har tsawon shekaru uku. A nashi bangaren ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Akbar Salihi ya bayyana jin dadinsa kan gagarumar rawar da kasar Masar ta taka a lokacin shugabancinta na kungiyar 'yan ba ruwanmu ta NAM. A safiyar yau talata ce aka bude zaman taron ministocin harkokin wajen kasashen da suke mambobi ne a kungiyar 'yan ba ruwanmu ta NAM, inda wakilan kasashe fiye da 80 suka halarci zaman a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran.
1087022





captcha