Bangaren siyasa, jamhuriyar muslunci ta Iran ta karbi ragamar shugabancin kungiyar kasashen yan ba ruwanmu a hukumance daga yau bayan da mataimakin ministan harkokin wajen kasar Masar ya mika ragamar shugabancin ga ministan harkokin wajen kasar Ali Akbar salihi a yau a wajen taron.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa a cikin gida, cewa jamhuriyar muslunci ta Iran ta karbi ragamar shugabancin kungiyar kasashen yan ba ruwanmu a hukumance daga yau bayan da mataimakin ministan harkokin wajen kasar Masar ya mika ragamar shugabancin ga ministan harkokin wajen kasar Ali Akbar salihi a yau a wajen taron da ake gudanarwa a Tehran.
A hukumance jamhuriyar Musulunci ta Iran ta karbi ragamar jagorancin kungiyar 'yan ba ruwanmu ta NAM a yau talata. A jawabin da ya gabatar a yayin bude zaman taron ministocin wajen kasashen kungiyar 'yan ba ruwanmu ta NAM a birnin Tehran na kasar Iran wakilin minsitan harkokin wajen kasar Masar Ramzi Izzuddin Ramzi ya jinjinawa kasar Iran kan gagarumin shirin da ta yi na karbar bakwancin zaman babban taron kungiyar 'yan ba ruwanmu ta NAM da tsara zaman taron ta hanyar da ta dace.
Matimakin ministan harkokin wajen Masar a ci gaba da jawabinsa ga mahalarta zaman taron na kungiyar 'yan ba ruwanmu ta NAM Ramzi Azzuddin ya mika ragamar jagorancin kungiyar ta 'yan ba ruwanmu ta NAM ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran, inda kasar ta Iran zata shugabanci kungiyar har tsawon shekaru uku. A nashi bangaren ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Akbar Salihi ya bayyana jin dadinsa kan gagarumar rawar da kasar Masar ta taka a lokacin shugabancinta na kungiyar 'yan ba ruwanmu ta NAM.
Da safiyar yau talata ce aka bude zaman taron ministocin harkokin wajen kasashen da suke mambobi ne a kungiyar 'yan ba ruwanmu ta NAM, inda wakilan kasashe fiye da 80 suka halarci zaman a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran.
1086837