Bangaren kasa da kasa, ma’aikatar kula da harkokin addinin muslunci ta kasar Syria ta tabbatar da kisan gillar da wasu yan ta’adda suka yi kan wani limamin masallacin juma’a acikin birnin Damascus wanda ya kasance daya daga cikin masu kira zuwa ga zaman lafiya da fahimtar juna ttsakanin al’ummar kasar.
Kamfanin dillancinlabaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alivenet, cewa ma’aikatar kula da harkokin addinin muslunci ta kasar Syria ta tabbatar da kisan gillar da wasu yan ta’adda suka yi kan wani limamin masallacin juma’a acikin birnin Damascus wanda ya kasance daya daga cikin masu kira zuwa ga zaman lafiya da fahimtar juna ttsakanin al’ummar kasar da kuma nuna rashin amincewa da duk wani aiki na ta’addanci.
Shugaban jam’iyyar Rasha demokradiyya ya sheda cewa bababr manufar taya da fitina acikin kasar Syria ita ce raunana kariyar da iran take da ita ta hanayawr kawancenta da gwamnatin Syria da suke baiwa gwagwarmayar palastinawa kariya da kuma ta Lebanon wanda ke bakantawa yammacin da karnukan farautarsu musamman ma daga cikin larabawa.
kungiyar alkaida ta ce ita ke da alhakin kai harin ta’addancin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da sukahada da fararen hula da jami’an tsaro a kasar Syria da sunan jihadi a tafarkin Allah kamar yadda kungiyar wadda ta shahara da irin wadannan ayuka ta sheda lamarin da ya fuskanci gagarumar suka da Allawadai daga al’ummomin duniya.
A nasa bangare dan majlaisar dokokin kasar Lebanon daga gugun ‘yan majalisa na kungiyar hizbullah Nawwaf Musavi ya yi kira da a warware matsalar kasar Syria ta hanyar lumana maimakon kara zuzuta wutar rikicin da ake gani yanzu haka daga wasu kasashen larabawa.
1086792