Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, shugaban kasar Masar ya bayyana cewa za su yi iyakacin kokarinsu domin ganin an kafa sabuwqar kasar palastinu mai cin gishin kanta tare da tabbatar mata da ku8jera a majalisar dinkin duniya amatsayin kasa ya kuma bayyana hakan a ne a taron kungiyar yan baruwanmu da ake gudanarwa tunkwanaki hudu.
A nasa bangaren babban sakataren majalisar dinkin duniya ya nuna goyon bayansa ga shirin Iran na makamshin nukiliya domin ayyukan farar hula, tare da yin fatan ganin an warware takaddamar da ake yi kan shirinta cikin yan lokuta masu zuwa.
Ban Ki Moon ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a gaban babban taron shugabannin kungiyar yan baruwanmu da halin yanzu haka yake ci gaba da gudana a nan birnin Tehran, inda ya jaddada cewa kasar Iran kasa mai muhimamnci a dukkanin bangarori na siyasar duniya da kuma yankin gabas ta tsakiya, wadda ke taka gagarumar rawa wajen warware da dama daga cikin matsaloli da suka addabi al’ummomin yankin, saboda haka ba za ta taba zama saniyar ware ba.
A nasa bangaren pira ministan kasar India Manmohan Sing a lokacin da yake gabatar da nasa jawabin, ya ce India za ta taimaka ma Iran matuka wajen ganin ta samu narasa wajen gudanar da dukkanin ayyuka da suka rataya kanta a matsayin kasar ta na sabuwar shugabar kungiyar ta NAM.
1088025