Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin jagoran juyin juya hali cewa, jagoran ya bayyana kasar Indiya a matsayin wata kasa mai karfi da kuma muhimmanci sannan ma'abociyar ci gaba a fagen ilimi da tattalin arziki daga nan sai ya kara da cewa: al'ummar Iran bayan nasarar juyin juya halin Musulunci musamman cikin shekarun baya-bayan nan sun gudanar da ayyuka daban-daban a fagen ilimi, tattalin arziki da zamantakewa, wanda mai yiyuwa ne ba a taba ganin irinsa ba tsawon karnin da ya gabata.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa dukkanin fagagen karfafa alaka ta dukkanin bangarori tsakanin kasashen Iran da Indiya a shirye suke yana mai cewa: alaka tsakanin kasashen biyu musamman a fagagen kasuwanci da ci gaban kasa za ta iya zama alaka karfafaffiya kuma mai kwantar da hankali.
Har ila yau kuma yayin da ya ke ishara da cewa alaka ta kasa da kasa dai ba abu ne abin dogaro da shi sosai ba, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Daya daga cikin irin wadannan kawaye na kasa da kasa wacce ba za a iya dogaro da ita ba, ita ce kasar Amurka wacce babbar kawa a wajenta kuma abar yarda ita ce gwamnatin yahudawan sahyoniya.
Haka nan kuma yayin da yake magana kan batutuwan da suka shafin wannan yanki ciki kuwa har da batun kasar Siriya da Afghanistan, Jagoran ya bayyana cewar mahangar Iran da Indiya kan wadannan lamurra sun yi kama da juna don haka sai ya ce: kasashen biyu suna iya karfafa alaka da aiki tare da ke tsakaninsu cikin lamurran da suka shafi wannan yankin.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar kwanciyar hankali, ‘yanci da kuma ci gaban kasar Indiya wani lamari ne mai muhimmanci ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran don haka sai ya bayyana fatan cewa: Iran tsawon wadannan shekaru uku na shugabancin kungiyar ‘yan ba ruwanmu, har ila yau kuma ta hanyar aiki kafada da kafada da kasar Indiya za ta sami damar karfafa wannan kungiya cikin batutuwan da suka shafi kasa da kasa da kuma wannan yankin.
Shi ma a nasa bangaren firayi ministan kasar Indiya Manmahon Singh wanda shugaban kasar Iran Dakta Mahmud Ahmadinejad ya ke wa jagoranci ya bayyana farin cikinsa mai yawan gaske da samun damar ganawa da Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran. Har ila yau kuma yayin da ya ke ishara da irin tsawon tarihi da kyakkyawar alaka ta al'adu da ci gaba da ke tsakanin al'ummomin kasashen Iran da Indiya, firayi ministan na Indiya ya ce: kasar Indiya tana fatan ganin alakarta da Iran ta kara bunkasa a bangarori daban-daban ciki kuwa har da fagen makamashi da abubuwan gina kasa.
Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da tattaunawarsu da shugaban kasar Iran ya kara dacewa: a yayin wannan ganawar an cimma wasu yarjejeniyoyi masu kyaun gaske a fagagen karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu.
1088182