Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ofishin jagora cewa, alokacin da yake ganawa da shugaban kasar Pakistan ya tabbatar da cewa kungiyar kasashen yan ba ruwanmu za ta iya taka gagarumar rawa a bangaren yaki da ta’addamnci da ake yi da sunan addinin muslunci wanda hakikanin gaskiya aiki ne ya yi hannun riga da koyarwar dukkanin addinai na sama kuma hakan ya kawo rashin amincewa da juna tsakanin al’ummomin duniya baki daya musamman ma awannan zamani.
A daya waje jagoran, ya bayyana cewa samun nasarori da ci gaban da kasar Iraki za ata yi don tabbatar da matsayinta tsakanin kasashe na iya fuskanatar wasu yan matsaloli, wanda ko dole ne kafin duk wata kasa ta samun yancin kanta da ci gaba da tabbatar da matsayinta tana bukatar shiri na gari da halin da zai sa ta cimma guri wanda mafi mahimmanci daga ciki sune ci gaban kimiya, da sake gina kasar hade da kayutata hanyoyin biya ma jama'ar kasar bukatocinsu, a game da hakan jagoran ya bada misali da kasar Iran, musamman a kan ci gaban kimiya da kasar ta samu da ma wasu sauren ci gaban da ma ba a taba tsamanin samunsu ba.
Al halin kasar Iraki ce tushen masanan kimiyan kasashen larabawa, don haka yake ganin ya dace da a samu wani yunkuri na masanan kimiya da zai hada daukacin masana da futattun mutane wanda za su iya samar ma jama'ar kasar ta Iraki kyakyawar rayuwa.
Praminitan kasar ta Iraki, Nuri Al-Maliki, ya nuna jin dadinsa sosai da suka gana da jagoran, inda ya tabbatar da cewa da yardar Allah, hulda tsakanin kasashen biyu za ta dore a kan fannoni da dama, inda tuni dama bangarorin yan kasuwa da kamfanoni ke zarya tsakanin kasashen biyu.
1088517